Shirin bayar da bashin karatu ga ɗalibai ba mai ɗorewa ba ne - ASUU

 


Kungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya sauya dokar ba da bashin karatu ga dalibai da ya amince da ita, zuwa tallafin karatu domin bai wa ɗalibai masu ƙaramin ƙarfi damar samun ilmi mai zurfi.


A wata hira da da gidan Talbijin na Channels ranar Lahadi, shugaban ASUU ya ce bashin karatun ba abu ne mai yiwu ba. A cewarsa, bayar da bashi don yin karatu "ba zai dore ba".


Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce, “tunanin bayar da bashin karatu ga dalibai ya zo ne a 1972 kuma yana cikin harkokin bankuna da aka kafa".


Ya yi iƙirarin cewa mutanen da suka karɓi bashin, ba su taɓa biya ba, kuna iya zuwa ku bincika. A shekarar 1994 ko 1993, sojoji sun kafa dokar soja mai lamba inbda suka kafa hukumar bayar da bashi ga ɗalibai. Sai Majalisar dokoki ta daidaita ta a shekara ta 2004 kuma a cikin shekara ɗaya, ta wargaje. Kuɗaɗen suka bace. Muna so mu ga yadda wannan zai bambanta".


A cewarsa, akwai dalibai sama da miliyan daya a jami’o’in gwamnatin Najeriya kuma rancen ba zai iya biyan kudin karatun dalibai ba.


A ranar Litinin ne Shugaba Tinubu ya sa hannu a kan dokar ba da bashi ga dalibai domin cika alƙawarin da ya dauka a lokacin yaƙin neman zabensa.


Shugaban majalisar wakilai ta 9, Femi Gbajabiamila, wanda yanzu shi ne shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa ne ya dauki nauyin gabatar da ƙudurin dokar a majalisa.


Dokar ta tanadi ba da bashi maras ruwa ga daliba masu ƙaramin ƙarfi a Najeriya.

Comments